An samu tashin 'bama-bamai' a Kano

Labari da dumi-dumi Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Najeriya na fuskantar matsaloli na tsaro daban-daban

An samu tashin wasu abubuwa da ake zaton bama-bamai ne a sassa daban-daban na birnin Kano ciki har da hedikwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ta daya da ke Kano.

Wuraren da bama-baman suka tashi sun hadar da caji ofis din 'yan sanda na marhaba da wani caji ofis din da ke Unguwa uku.

Wakilin BBC a garin ya ce kuma an ji karar harbe-harben bindigogi bayan tashin bama-baman abinda ya jefa mutanen da ke yankunan da bama-baman suka tashi cikin rudani.

Ana kuma iya ganin hayaki na tashi a wuraren da bama-baman suka tashi.

Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fama da hare-hare a sassa dabam-daban na kasar.

Kawo yanzu ya tabbatar da hari a kan ofisoshin 'yan sanda a Arewaci da tsakiya da kuma Kudancin birnin.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AP ya ce fashewar ta yi karfin da har sai da girgiza motarsa wacce ke da nisan mil da dama daga wurin.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki nauyin harin, amma a 'yan kwanakin nan kungiyar Boko Haram ta matsa kaimi wurin kai hare-hare a sassan kasar da dama cikin har da ofishin Majalisar dinkin duniya da ke Abuja.

Karin bayani