Rick Perry, dan takarar shugabancin kasa a Amurka, ya janye

Rick Perry Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gingirich ya kara samun karfi

Gwamnan jihar Texas a Amurka, Rick Perry, ya janye takararsa a zaben da jam'iyyar Republican ke yi don fitar da mutumen da zai tsaya mata a zaben shugaban kasa da za a yi a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Ya ba da sanarwar ce a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a jihar South Carolina ta Amurkar.

Mr Perry ya ce, “Da na yi tunani a kan makomar wannan yakin neman zabe, na yanke shawarar cewa babu wata hanya mai fa'ida a gare ni dangane da wannan batu, saboda haka na dakatar da yakin neman zabena.”

Mr Perry ya goyi bayan daya daga ciki 'yan takarar na jam'iyyar ta Republican, Newt Gingrich, wanda ya bayyana da cewa mutum ne mai ra'ayin rikau da kuma hangen nesa.

A farkon yakin neman zaben dai, an yi ta karrama Mr Perry din, amma wakilin BBC ya ce ya gaza wajen baza farin jininsa a duk fadin Amurka.

Karin bayani