'Yan takarar Republican sun yi yunkurin karshe a muhawara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan takarar Jam'iyyar Republican hudu da su ka rage

Mutane hudun da suka rage a fafutukar tsayawa jam'iyyar Republican takara a zaben shugaban kasar Amurka sun yi yunkurinsu na karshe na gamsar da masu zabe a wata muhawarar da aka nuna ta talabijin a Jihar South Carolina, inda za a gudanar da zaben fidda gwani mai muhimmanci ranar Asabar.

Tsohon kakakin majalisar Wakilai Newt Gingrich ne dai ya bude muhawarar inda cikin fushi ya musanta rahotannin da kafofin yada labarai suka ba da cewa ya taba yarjejeniya da tsohuwar matarsa cewa ko wannensu na iya yin jima'i da wani ko wata a waje.

Mista Gingrich ya ce bai taba tunanin akwai wani abin kaico ba da ya kai dauko batun tsohuwar matarsa a mai da shi wani muhimmin batu a yakin neman zabe ana saura kwanaki biyu a gudanar da zaben fidda gwani.

Batun da jama'a su ka fi mayarda hankali akai a muhawarar da aka yi a South Carolina shine tambayar da aka yi wa dan takara Newt Gingrich.

Farin jini

Newt Gingrich ya fusata ne a lokacin da alkalin muhawarar ya tambayesa ko ya bukaci tsohuwar matarsa ta bari ya rika jima'i a waje da wata mata, matar da daga baya kuma ya aura.

Sauran abokan takararsa dai sun kaucewa batun ganin cewa tambayar da alkalin ya yiwa dan takarar zai taimaka musu wajen rage masa farin jini.

Mista Gingrich ya fara tasiri a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi na baya bayanan kuma akwai rahotannin dake nuni da cewa, zai iya wuce dan takarar jam'iyyar dake kan gaba, wato Mitt Romney.

Ana dai ganin wannan batu zai shafi farin jinin Gingrich a yankin South Carolina ganin cewa masu jefa kuri'a a yankin 'yan ra'ayin rikau ne.

Idan kuma har Mitt Romney ya lashe zaben fidda gwanin da za'a yi a ranar asabar, zai karfafa matsayarsa na kalubalantar shugaba Obama.

A jiya ne dai gwamnan Texas, Rick Perry ya janye takararsa karkashin inuwar jam'iyyar Republican din.

Karin bayani