Wasu abubuwa sun farfashe a Kano

Kano Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kawo babu cikakken bayani kan barnar da lamarin ya haifar

Wasu abubuwa kimanin 20 sun farfashe a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya

Wailin BBC Yusuf Yakasai a birnin na Kano, ya ce garin ya rikide inda jama'a ke ta kokarin neman mafaka.

Ana kyautata zaton daya daga cikin fashewar ta afku ne a ofishin 'yan sanda na jihar.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan barnar da lamarin ya haifar.

A baya kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare makamantan wadannan a sassan kaasar da dama.