Hare-haren bama-bamai sun rikita birnin Kano

Labari da dumi-dumi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Boko Haram ta dade tana kai hare-hare a Najeriya

Rahotanni sun ce mutane ne da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren bama-bamai da suka tashi a sassa daban-daban na jihar Kano a Arewacin Najeriya.

Fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda biyu a babban ofishin 'yan sanda na kasa shiyyar Kano, an kuma kai wasu karin hare-haren a wasu ofisoshin 'yan sanda a birnin.

Wani jami'in 'yan sanda a wurin ya shaida wa BBC cewa dan kunar bakin wake ne ya kai harin - inda mutane uku suka rasa rayukansu.

Mai magana da yawun Hukumar shige da fice reshen jihar Kano Mohammed Kanoma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa an kashe jami'ansu guda uku.

Gidan talabijin na Channels mai watsa shirye-shiryensa daga Legas ya ce daya daga cikin masu aiko masa da rahotanni (Enenche Akogwu) na daga cikin wadanda suka mutu a harin.

Fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda biyu a babban ofishin 'yan sanda na kasa shiyyar Kano, an kuma kai wasu karin hare-haren a wasu ofisoshin 'yan sanda a birnin.

Mahukunta a jihar ta Kano sun kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a ko'ina cikin jihar.

Kungiyar Boko Haram ta dauki nauyin alhakin harin bama-baman. Kungiyar ta sha kai hare-hare a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce bama-baman sun fara tashi ne da misalin karfe 5 na Yamma, kuma an ji karar harbe-harben bindigogi bayan tashin bama-baman abinda ya jefa mutanen da ke yankunan da bama-baman suka tashi cikin rudani.

Ya kara da cewa harin ya zowa mazauna garin da mamaki ganin cewa ba su saba ganin irin wadannan hare-hare ba.

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Najeriya na fuskantar matsaloli na tsaro daban-daban

Ana kuma iya ganin hayaki na tashi a wuraren da bama-baman suka tashi.

Rahotanni sun ce ana musayar wuta a babban ofishin 'yan sanda na jihar da ke Bompai. Sannan aka kai karin hare-hare a ofisoshin 'yan sanda na Yar Akwa da Unguwa Uku.

"An shafe sa'o'i biyu ana musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da jami'an leken asiri na SSS a babban ofishinsu da ke Unguwar Nasarawa," kamar yadda wani mazaunin unguwar ya shaida wa BBC.

Wani da ya shaida lamarin ya shaida wa BBC cewa ya ga ana debo wadanda abin ya ritsa da su amma ba shi da tabbas ko sun mutu ko kuma sun jikkata.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AP ya ce fashewar ta yi karfin da har sai da girgiza motarsa wacce ke da nisan mil da dama daga wurin.

Daukar alhaki

Kungiyar Boko Haram wacce ta sha kaddamar da hare-hare a kasar ta ce ita ce ta kai harin.

Mai magana da yawun kungiyar ta Boko Haram Abu Qaqa, ya shaida wa 'yan jarida a Maiduguri cewa "kungiyar ce ta kai harin bayan da ta nemi a saki 'ya'yanta da aka kama amma hukumomi suka ki".

"Gwamnati ta kafa dokar hana zirga-zirga ta sa'o'i 24 domin tabbatar da tsaro a jihar," a cewar kwamishinan yada labarai na Kano Dr Faruk Jibril.

Masu sharhi na cewa wannan shi ne hari mafi girma da kungiyar ta kai a lokaci guda, kuma mafi girma a jihar ta Kano.

Kungiyar ta zafafa hare-hare a bara, inda ta nufi hedkwatar 'yan sanda da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja.

A 'yan kwanakin nan an sha kai hare-hare kan mabiya addinin Kirista a Arewa da kuma kan Musulmai wasu sassan Kudancin kasar.

Karin bayani