Jonathan ya yi Allah Waddai da hare-haren Kano

Shugaba Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan na Najeriya

Fadar shugaban Nigeria, Goodluck Jornathan ta fidda sanarwa game da hare-haren da aka kai a Kano wadanda suka yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

A cikin sanarwar shugaban Nigeriar, ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasu kuma ya ce zai tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan danyen aiki sun fuskanci hushin hukuma.

Shi ma sakataren kula da harkokin wajen Birtaniya yayi Allah wadai da harin, yana mai cewa duniya ba za ta bata amincewa da irin wadannan ayyukan asha ba.

Karin bayani