Mutane akalla dari da hamsin ne suka hallaka a Kano

Hare-haren bam din da aka kai a Kano
Image caption Hare-haren bam din da aka kai a Kano

Rahotanni daga birnin Kano dake Arewacin Najeriya na cewar kawo yanzu, mutane akalla dari da hamsin ne suka rasa rayukansu a sakamakon jerin hare-haren bama baman da aka kai jiya a Kano, inda yanzu haka aka tara gawawwakinsu a asibitin Murtala da ke birnin Kano.

Sai dai har yanzu hukumomi ba su fito suka fadi ainihin adadin wadanda suka hallaka ba.

A yau dai an wayi gari cikin dokar hana fita, inda ma'aiaktan agaji ke ci gaba da tattara wadanda hare-haren suka rutsa da su.

Wadanda suka shaida al'ammarin, sun ce a wasu daga cikin wuraren da aka kai hare-haren, yan kunar bakin wake ne, wasu ma cikin motoci makare da nakiyoyi suka kai hare haren.

Kungiyar nan ta Ahli sunna Lid Daawati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram ta ce ita ce ta kai hare haren.

Karin bayani