An tabbatarwa da shugaba Saleh na Yemen kariya

'Yan majalisar dokokin Yemen Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan majalisar dokokin Yemen

Majalisar Dokokin Yemen ta jefa kuri'ar amnicewa da baiwa tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh kariya daga gurfana a gaban alkali.

Wakilin BBC yace kudirin dokar ya baiwa tshohon shugaban kasar cikakkiyar kariya akan duk abunda ya yi a tsawon mulkin sa na shekaru 34.

An dai jinkirta kudirin dokar ne, saboda jama'a sun nuna adawar su da irin wannan kariyar da aka baiwa wasu mukarrabansa.

A kwanakin baya ne Ali Abdalla Saleh ya amince da wata yarjejeniyar sauka daga karagar mulki.

Karin bayani