Bama bamai sun tashi a Bauchi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani waje da bama-bamai suka kona a Najeriya

A Najeriya, rahotanni daga jihar Bauchi na cewa an samu tashin wasu abubuwa da ake zaton bama-bamai ne tare da jin karar harbe-harben bindigogi a safiyar ranar Lahadi a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishin 'yan sandan jihar, Okechuku Aduba, ya shaidawa BBC cewa nakiyoyi ne suka tashi a garin Bauchi, da Tafawa Balewa da kuma Marabar Liman Katagum.

Wani ganau a Tafawa Balewa ya tabbatarwa da BBC cewa ya ga wata yarinya ta kone sakamakon tashin bama baman.

Har yanzu dai ba a tabbatar da wadanda suka tashi bama baman ba, sai dai Mr Aduba ya ce rundunarsa na gudanar da bincike game da batun, kuma za su yiwa manema labarai karin bayani da zarar sun kammala.

Kakakin gwamnatin jihar, Mr Ishola Micheal, ya ce karar fashewar da aka ji a Bauchi ta faru ne sakamakon fashewar wadansu na'urorin ba da wutar lantarki.

Karin bayani