Sojojin sun keta Hakkin BilAdama a Masar- HRW

Jami'an tsaro suna tursasa wa wata mai zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto r
Image caption Jami'an tsaro suna tursasa wa wata mai zanga-zanga a Masar

Rahoton shekara-shekara na kungiyar kare Hakkin BilAdama ta Human Rights Watch, ya ce baa samu kyautatuwar al'ammura a fannin kare Hakkin BilAdama a Masar ba, tun bayan da aka kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a bara.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce a gaskiya, halin da ake ciki ya ma kara muni.

Hakazalika, kungiyar ta soki lamirin gwamnatocin kasashen waje bisa gazawar da suka yi wajen kawo goyon baya ga masu zanga-zangar neman kawo sauyi a kasashen Larabawa.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce akwai bukatar kasashen su yi amfani da tasirin da suke da shi wajen tabbatar cewa sabbin gwamnatocin kasashen Larabawa sun yi aiki da doka da oda da kuma mutunta Hakkin BilAdama, musamman ma na maata da kabilu marasa rinjaye.

Karin bayani