Wani babban jami'in gwamnatin Libya zai ajiye akinsa

Abdelhafiz Ghoga Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abdelhafiz Ghoga

Mataimakin shugaban gwamnatin wucin gadin Libya, Abdelhafiz Ghoga ya ce zai yi yi murabus saboda yawan zanga zangar nuna adawa da shi da ake yi a Benghazi, birni na biyu mafi girma a Kasar.

Wakilin BBC ya ce bayan an kwashe kusan makonni biyu ana zanga zanga a Banghazi, yanzu gwamnatin wucin gadin kasar na sa ran wannan murabus din zai rage matsin lambar da ta ke fuskanta.

Shi dai Adelhafiz Ghoga yana kula da mutane da dama, kuma masu zanga zanga sun ce yana da kusanci da tsohuwar gwamnatin Gaddafi.

Abdel Hafiz Ghoga ya shaidawa gidan telbijin na Aljazeera cewa zai yi murabus saboda kare bukatun kasar.

Karin bayani