Saudiyya ta nemi da a kara matsa lamba a kan Syria

Saud Al faisal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saud Al faisal

Kasar Saudiyya ta ce za ta janye 'yan kasar ta dake cikin tawagar masu sa idon da kungiyar kasashen larabawa ta tura Syria.

Ministan Harkokin wajen Saudiyyan, Saud Al faisal, ya ce Syria ba ta mutunta alkwarin ta ba, a karkashin yarjejeniyar da ta cimma da kasashen Larabawa.

A watan jiya ne aka kulla yarjejeniyar, wadda a karkashinta ne aka tura tawagar sa idon a yunkurin kawo karshen zubda jinin da akeyi a kasar.

Wakilin BBC ya ce ministan ya yi kira ga kasashen duniya da su bi duk hanyar da ta dace don matsa wa Syria lamba.

Ministan harma ya ambaci wasu kasashe masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, abun da ake ganin wata alama ce dake nuna cewa yana son Rasha da China su yi amfani da karfin su na fada a ji a majalisar wajen matsawa Syria lamba.

Karin bayani