'Yan Taliban sun hallaka wasu sojojin Pakistan

Wasu mayakan Taliban Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu mayakan Taliban

Mayakan Taliban a Pakistan sun fidda wani hoton bidiyo da ya nuna yadda su ka kashe wasu sojojin Pakistan 15.

An kame sojojin ne a wani farmaki da aka kai akan wani wurin binciken ababen hawa dake kusa da birnin Tank na arewacin kasar.

An gano gawarwakin ne kwanaki kadan bayan an kai farmakin.

A hoton bidiyon mai tsawon minti biyu, an nuno yadda aka harbe mutanen da bindiga bayan an rufe idanun su.

An kuma ji wani kwamandan Taliban din yana cewa ai kisan sojojin, ramuwar gayya ce ga kisan wasu dakarun su goma sha biyu da aka yi.

Wani jami'in soja ya tabbatar da cewa wadanda aka kashe din sojojin Pakistan ne.

Karin bayani