An fara bincike akan kudaden tallafin man fetur a Najeriya

Hakkin mallakar hoto google

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, ta soma binciken manyan kamfanonin dake hada-hadar man fetur a cikin kasar, wadanda suka ci gajiyar kudin tallafin man fetur da gwamnati ta ce ta kashe a shekarar da ta wuce.

Hukumomin kasar sun ce kusan Naira triliyon daya da biliyon dari uku ne aka biya a matsyain tallafi.

Gwamnatin kasar ce dai ta umurci hukumar EFCC da ta gudanar da bincike akan badakalar da ake zargin na faruwa a game da tallafin man petur din.

A kwanankin baya anyi yajin aikin da kuma jerin zang zanga don nuna adawa da janye tallfin a Najeriya.

A lokacin zanga zangar dai wasu 'yan kasar sun nace akan lalle sai an bincike kamfanonin da ke hada-hadar man.

Karin bayani