Tarayyar Turai za ta sanya takunkumi akan Iran

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar tarayyar Turai ta amince da wasu tsauraran matakan takunkumi akan Iran saboda zargin da akewa kasar na yunkurin kera makaman nukiliya.

Matakan sun hada da haramta sayen danyen man Iran da kuma hana taba kadarorin da babban bankin kasar ya mallaka.

Tarayyar Turai dai na sayen kimanin kashi ashirin cikin dari na man fetur din da Iran ke fitarwa zuwa kasashen waje.

Sai dai Iran ta yi barazanar rufe mashigin Hormuz idan aka kakaba mata takunkumin.

Wannan batu ya janyo tashin farashin danyen mai zuwa kusan dalar Amurka dari akan kowane gangan danyen mai a kasuwar danyen mai ta New York.