Akalla mutane '185 aka kashe a Kano'

Akalla mutane '185 aka kashe a Kano' Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ne hari mafi girma da Boko Haram ta kai a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce, mutane 185 ne suka rasa rayukansu, a hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a ranar Juma'a.

Haka kuma 'yan sandan sun ce, sun gano wasu daruruwan bama-bama da kuma motoci kimanin goma makare da bama-baman, a wurare dabam-daban a jihar.

Tunda farko a ranar Litinin shugabanni a jihar sun jagoranci addu'o'i na neman zaman lafiya.

"Alkaluman da ke gabanmu sun nuna cewa 'yan sanda 29 da jami'an SSS 3 da na hukumar shige da fice 2 da kuma farar hula 150 ne suka rasa rayukansu a harin," a cewar wata sanarwa da kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano Ibrahim Idris ya sanya wa hannu.

A ranar Juma'a ne wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin 'yan sanda da na sauran jami'an tsaro a jihar - abinda ya jefa birnin na Kano - wanda shi ne mafi girma a Arewacin kasar cikin dimuwa.

Afuwa ga 'yan Boko Haram

A ziyarar da suka kai birnin na Kano domin jajanta lamarin da ya faru, shugabannin majalisar dokokin Najeriya sun nemi da a yiwa 'ya'yan kungiyar Boko Haram afuwa bisa hare-haren da suke kaiwa a kasar a matsayin wata hanya ta yin rigakafin aukuwar irin haka a nan gaba.

Shugaban Majalisar wakilai ta kasar Aminu Tambuwal ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar a yiwa 'ya'yan kungiyar afuwa bisa abubuwan da suka aikata, domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Shi ma a nasa bangaren shugaban majalisar dattawa na kasar Sanata David Mark, ya yi kiran da a yafewa wadanda suka kai hare-haren na Kano, a matsayin wata hanya ta yin rigakafin aukuwar irin haka a nan gaba.

Sai dai kalaman na su na zuwa ne bayan da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ce a shirye hukumomin tsaro suke "su murkushe masu kai hare-haren ta'addanci a kasar".

Addu'ar zaman lafiya

An nemi al'umar Musulmi da Kirista a jihar ta Kano da su gudanar da addu'o'i domin samun zman lafiya.

Tuni aka gudanar da addu'o'i na musamman a kusa da fadar mai Martaba Sarkin Kano, domin bukatar Allah ya taimaka wajen kawo karshen tashe-tashen hankula.

Jami'an 'yan sanda sun ce an gano bama-bamai 12 kirar gida a wata mota da aka ajiye a birnin.

Likitoci sun ce ana ci gaba da kawo gawarwaki zuwa mutuware kuma adadin wadanda suka mutu sakamakon harin za su iya karuwa.

'A kawo karshen tashin hankali'

Wakilin BBC a Kano ya ce wasu mutane sun fara komawa ayyukansu na yau da kullum, amma akwai dinbin jami'an tsaro a kan tituna. Akwai kuma dokar hana yawon dare.

Gwamnatin Kano da fadar Sarki ne suka kira da a gudanar da addu'o'i a gidajen rediyon jihar.

An umarci duka Musulmi da Kirista su gudanar da addu'o'i a wuraren ibadarsu.

Wakilinmu ya ce akalla mutane 200 ne suka halarci addu'a a babban masallacin birnin, yayin da aka gudanar da addu'o'in a sauran masallatai na birnin.

Birnin Kano ne mafi girma a arewacin Najeriya inda Musulmai suke da gagarumin rinjaye, amma akwai mabiya addinin Kirista 'yan kadan.

Karin bayani