ICC za ta binciki manyan 'yan siyasar Kenya

Kotun ICC Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan kudin Kenya Uhuru Kenyatta a kotun ICC

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC, t ace biyu daga cikin mutanen da ke neman shugabancin kasarKenyaza su fuskanci shari’ar cin zarafin bil’adama biyo bayan zaben shugaban kasar na shekara ta 2007.

Ministan kudi Uhuru Kenyatta da tsohon minister William Ruto duka na fuskantar zargin aikata ba dai dai ba.

Suna cikin manyan jami’an Kenya hudu – duka sun musanta zargin da ake yi musu.

Sai dai kotun bata tabbatar da zargin da ake yi wa wasu jami’an biyu ba.

An yi taho-mu-gama tsakanain magoya shugaba Miu Kibaki da na abokin hamayarsa, Raila Odinga ne a lokacin da ake sanar da sakamakon zaben.

Fiye da mutane dubu ne suka mutu sannan wasu kusan rabin miliyan suka yi gudun hijira sakamakon hargitsin da ya biyo bayan zaben.

An kai batun gaban kotun ICC ne, bayan kotun ta aike da babban mai shigar da kararta, Luis Moreno Ocampo, zuwa kasar don gudanar da bincike game da abin da ya yi sanadiyar rikicin bayan zaben.

Luis Moreno Ocampo ya yi amannar cewa ba haka kwatsam rikice-rikicen bayan zaben kasar suka faru ba, illa dai wasu fitattatun 'yan siyasa ne suka kitsa su.

Fitacce daga cikin wadanda ake tuhuma shi ne Uhuru Kenyatta - wanda a halin yanzu shi ne mataimakin Firayim Minista, kuma dan shugaban kasar na farko ne.

Karin bayani