Shugaba Saleh ya fice daga Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ali Abdallah Saleh

Shugaban Yemen Ali Abdullah Saleh ya fice daga kasar kwana guda bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin da zai bashi cikakkiyar kariya daga fuskantar hukunci.

Bayar da kariyar na zuwa ne duk da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin shugaba Saleh da ake ci gaba da gudanarwa a kasar.

Jami'an gwamnatin kasar dai sun ce shugaban ya tafi kasar Oman, sai dai ana sa-ran zai je Amurka inda za a duba lafiyarsa.

Kafin tafiyar ta sa, Mr Saleh ya yi wa al'ummar kasar jawabi inda ya nemi afuwa game da kura-kuran da ya yi a tsawon shekaru talatin da ya shafe yana mulkin kasar.

Ya ce:''ina mika godiyata ga mazanmu da matanmu saboda yadda suka iya jurewa watanni goma sha daya na yunwa, da daukewar wuta, da rashin kayan more rayuwa da abubuwa da dama.Ina neman afuwa ga dukkanin 'yan kasar Yemen''.