Majalisar Faransa ta zartar da doka kan Turkiyya

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Nicholas Sarkozy

Majalisar dattawan Faransa ta zartar da wani kudurin doka da zai tuhumi mutane da aikata babban laifi idan suka musanta cewa Turkawa sun yi kisan kiyashi kan Armeniyawa a lokacin yakin duniya na daya.

Hakan na nufin duk wanda ya musanta batun kisan kiyashin zai iya fuskantar zaman gidan wakafi na shekara daya a Faransa.

Da ma dai akwai doka a Faransa wacce ta bayyana cewa kisan da aka yiwa Armeniyawa a Turkiya kisan kare-dangi ne.

Majalisar dattawan ta tsaurarata ne kawai ta hanyar fayyace hukuncin da mutum zai fuskanta.

Matakin zai kawo baraka

Idan shugaban Faransa, Nicholas Sarkozy, ya sanyawa dokar hannu batun zai kawo mummunar baraka tsakanin Faransa da Turkiya, wacce duk da yake ta amince cewa fiye da 'yan Armeniya miliyan daya ne suka mutu, sai dai ta sha musancewa cewa an yi kisan ne da zumar aiwatar da kisan kare-dangi.

Jakadan Turkiya da ke Faransa, Tahsin Bur-cuoglu, ya shaidawa manema labarai cewa zartar da wannan doka ba zai kasance alheri ga dukkan bangarorin ba.

Gwamnatin Turkiyya ta yi alkawarin sanyawa Faransa abin da ta kira takunkumi na din-din-din.

Sai dai Armeniya ta yi maraba da zartar da wannan doka, tana mai cewa ta dade tana sa rai da hakan.

Karin bayani