Ferguson ya nemi a yi da'a a Liverpool

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya rubutawa magoya bayan kungiyar Manchester da su nuna da'a a tattakin da kungiyar za ta kai Liverpool.

Manchester United za ta fafata da Liverpool ne a zagaye na hudu a gasar cin kofin FA.

Kocin United din dai ya bukaci magoya bayan kungiyar su nuna da'a kuma su ba kungiyar goyon bayan da ya kamata.

Ferguson ya rubuta wasika makamancin wannan a watan Okutoba a lokacin da kungiyoyin biyu su ka kara.