Ana ta jin harbe-harben bindiga a Kano

Ana ta jin harbe-harben bindiga a Kano Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akalla mutane 185 aka kashe a Kano ranar Juma'a

Rahotanni daga Kano na cewa ana jin karar harbe-harbe a cikin birnin wanda har yanzu ke kokarin murmurewa daga hare-haren bama-baman da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 185.

Mazauna unguwar Sheka sun ce da misalin karfe 6:30 ne wasu 'yan bindiga suka zo a mota sannan suka bude wuta kan wani ofishin 'yan sanda, kawo yanzu babu tabbas kan irin barnar da abin ya haifar.

Wakilin BBC a Kano ya ce akwai rahotannin da ke nuna cewa ana jin karar wau hare-harben a unguwar Bampai - wacce na daya daga cikin wuraren da aka kai hari ranar Juma'a.

Hakan na zuwa ne bayan wasu harbe-harben makamantan wannan da aka yi ta ji a ranar Litinin, har zuwa wayerwar gari.

'Allah ya kawo mana dauki'

Mazauna unguwar Hotoro sun shaida wa BBC cewa an shafe dare ana musayar wuta a unguwar.

Rahotanni sun ce hadin gwiwar jami'an tsaro ne suka zagaye wani gida da ake zargin wani dan kungiyar Boko Haram na zaune a ciki.

Daga bisani jami'an tsaron sun kashe mutumin tare da matarsa abinda ya kara jefa mazauna unguwar cikin wani yanayi na tashin hankali.

"Mun kwana ba mu yi barci ba, hatta kananan yara karar harbi ta hana su barci, muna cikin wani mummunan yanayi sai dai Allah kawai ya kawo mana dauki," kamar yadda wata mata a unguwar ta Hotoro ta shaida wa BBC.

Wannan tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta yi kira ga 'yan Najeriyar da su ci gaba da kasancewa tsintsiya-madaurinki-daya.

Hakkin mallakar hoto INTERNET
Image caption An gudanar da addu'ar neman zaman lafiya a jihar ta Kano

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanyawa hannu ta nemi 'yan kasar da "su hada kansu" a dai dai lokacin da ake fuskantar tashin hankalin da ke da alaka da addini.

A garin Maiduguri ma....

Hakazalika wani wakilin Amurkar da ya kai ziyara Najeriya ya yi alkawarin tallafawa kasar ta fuskar tsaro.

Wani rahoto da kungiyar kare hakkiin bil'adama ta Human Rights Watch ta fitar, ta ce kungiyar ta Boko Haram ta kashe kusan mutane 1,000 tun daga shekara ta 2009.

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno sun nuna cewar an samu fashewar bam a tsakiyar birnin, inda harbe-harben bindigogi suka biyo baya.

Mazauna tsakiyar birnin da dama sun tsere daga gidajensu yayin da wasu suke gudanar da sallar Isha'i, suka makale a cikin masallatai domin gudun abubuwan da ka iya biyo baya.

Kungiyar Boko Haram mai hedkwata a Maiduguri ta matsa kaimi wurin kai hare-hare a 'yan kwanakin nan - inda ta kashe mutane kusan 200 a birnin Kano ranar Juma'a.

Karin bayani