'Ba a yi harbe-harbe a Bompai ta Kano ba'

Mutanen da suka rasa rayukansu a harin 20 ga watan Janairu
Image caption Wadansu daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a harin 20 ga watan Janairu

Wata majiyar ’yan sandan Jihar Kano a arewacin Najeriya ta musanta cewa an kai hari a shiyyar Bompai a daren ranar Talata.

Mazauna shiyyar dai sun ce sun ji kararar harbe-harbe na kimanin mintuna 15 kafin a tsagaita.

Sai dai a cewar majiyar ta ’yan sanda wadansu jami'anta ne wadanda aka kawo daga wata jihar suka yi harbe-harben a iska don nuna cewa sun fa iso lafiya.

Harbe-harben dai, a cewar mazauna yankin na Bompai, sun yi matukar kidimasu, har ma sun yi zaton wani sabon harin ne aka kai hedkwatar ’yan sandan.

A unguwar Sheka ma dai an samu harbe-harben da jefa wasu abubuwa masu fashewa a ofishin ’yan sanda na unguwar, al’amarin da ya razana mazauna yankin da abin ya faru.

Wadansu rahotanni dai na cewa harin ya lalata ofishin, ko da yake hukumar ’yan sandan ba ta yi karin bayani ba a kan wadanda abin ya shafa.

Wadannan al'amura dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin al'umma a Jihar ta Kano suka gudanar da wani taro da Gwamnan Jihar da nufin lalubo musabbabin matsalar rashin tsaro da kuma yadda za a tunkareta.

Mafi yawan wadanda suka yi magana a wajen taron dai na ganin cewa kamata ya yi a tattauna da duk wadanda aka san suna da hannu wajen tashe-tashen hankulan.

Alhaji Magaji Danbatta ya shaidawa Wakilin BBC cewa:

“Ni shawarata [ita ce] gwamnati ta bincika ta ga menene ya haddasa wannan abin—idan Boko Haram din ne, su wanene Boko Haram; menene bukatunsu?

“Mun ji cewa suna kukan kashe musu shugabanni da kuma kama musu mutane da aka yi aka tsare ba da hakki ba.

“To don me gwamnatin ba za ta duba kukansu ba, ta yi maganin abin?”

A ganin Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule kuwa, rashin adalcin shuganni shi ne musabbabin matsalar ta rashin tsaro.

A cewarsa, “Duk al’amarin nan ya tsaya a kan shugabanci—Hausawa suna cewa salla daga liman take baci”; ya kuma kara da cewa, “Duk duniyar nan inda ka ga ana tashin hankali, in ka bibiya a karkashinsa za ka ga zalunci ne”.

Dimbin shuganni ne a jihar ta Kano suka halarci taron, ciki har da malamai da tsofaffin manyan jami'an tsaro, da sarakai, da ’yan kasuwa.

Hakan kuwa ya nuna cewa al’amarin na ranar Juma'a ya girgiza kowa a jihar.

Karin bayani