Obama ya fayyace kalubalen da ke gabansa

Barack Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama yayin da ya ke jawabi a gaban Majalisar Dokoki

Shugaba Barack Obama ya yi jawabi ga Amurkawa a kan halin da kasar ta ke ciki a gaban majalisar dokoki.

Shugaba Obama ya yi amfani da jawabin ne wajen fayyace abubuwan da yake fatan aiwatarwa idan Amurkawa suka sake ba shi damar darewa kujerar shugabancin kasar a watan Nuwamba.

A jawabin nasa, Shugaba Obama ya fi mayar da hankali ne a kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, da samar da ayyukan yi, da kuma ilimi, yana jaddada cewa babu kasar da ta kai Amurka daukaka a duniya.

A cewar Mista Obama, wajibi ne a farfado da fatan da ko wanne Ba-Amurke ke da shi na samun ci gaba a rayuwa.

“Batun da ya fi ko wanne muhimmanci a wannan zamani shi ne yadda za a raya wannan fata; babu wani kalubale, kuma babu wata muhawara da ya/ta fi wannan muhimmanci”, in ji Mista Obama.

Ya kara da cewa zai so ya ga an gina tattalin arzikin Amurka a kan tubali Mahdi-ka-ture; tattalin arzikin da a cewarsa Amurkawa za su gina da jibin goshinsu, ta hanyar bunkasa masana'antu da inganta makamashi.

Shugaban na Amurka ya kuma ce masana'antun kasar na ci gaba da daukar ma'aikata, har ma a watanni ashirin da biyun da suka gabata sun samar da ayyukan yi fiye da miliyan uku.

Mista Obama ya ce Amurka ta yi farar dabara da ta janye dakarunta daga Iraki ta mai da hankali gaAfghanistan, don kuwa hakan ya kara mata kuzari wajen kawar da makiyanta, musamman Usama bin Laden.

Shugaba Obama ya kuma yi watsi da ikirarin da wadansu ke yi cewa tasirin Amurka a duniya ya ragu.

A cewarsa, “Duk wanda ya ce Amurka ta ja baya ko tasirinta ya ragu bai san abin da yake yi ba”.

Daga nan sai Shugaba Obama ya yi kira ga abokan adawarsa su hada karfi da karfe don a gudu tare a tsira tare, amma ya kara da cewa zai yi adawa da duk wani yunkuri na sake dawo da manufofin da suka jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki.