Ko za a samu bore irin na kasashen Larabawa a Afrika?

Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a sassa da dama na Najeriya

A daidai lokacin da ake bukukuwan tunawa da boren da aka yi a kasashen Tunisia da Masar wanda ya kifar da gwamnatocin kasar, sannan ya haifar da bore a wasu kasashen Larabawa: Tambayar ita ce ko za a sami makamancin wannan boren a kasashen Afrika?

An kifar da gwamnatoci, masu mulkin kama-karya sun sha kasa, an watsa boren a gidajen talabijin ta hanyar da ba a taba tsammani ba watanni 12 da suka gabata.

Nahiyar Afrika na daga cikin sassan duniya da ke da shugabannin da suka dade suna mulkin kama-karya - kuma wannan shi ne abinda mazauna kasashen Larabawan ke adawa da shi.

Sai dai bore makamancin wannan a nahiyar Afrika zai mayar da nahiyar baya ne - maimakon ciyar da ita gaba.

A takaice ma zai kawo cikas ne kan nasarorin da wasu kasashen suka samu a shekarun 1980 da kuma farkon 1990 - lokacin da suka kawar da masu mulkin kama-karya domin gudanar da zabuka na jam'iyyu da dama.

'Azzaluman shugabanni'

Sai dai, kada kuri'a kadai ba zai wadatar ba - kuma demokuradiyya bata kare a kada kuri'a ba kawai, kamar yadda kasashen Tunisia da Masar suke kokarin lalubo mafita bayan juyin-juya halin da aka yi.

Babu wata kasar Larabawa da ke da ikon gudanar da zanga-zanga ko kalubalantar gwamnatocinsu kafin boren da aka yi a Tunisia a ranar 14 ga watan Janairun 2011.

Zanga-zangar da aka gudanar a watan Yulin shekara ta 2011 a kasar Malawi, ba an shirya ta bane domin kifar da gwamnati ko neman shugaba Bingu wa Mutharika ya yi murabus ba.

Ana korafi ne game da tabarbarewar tsarin demokuradiyya wanda ya baiwa gwamnati mai ci damar yin mulki ba tare da wani kalubale ba.

Haka lamarin yake a Najeriya - baya ga rikicin kungiyar Boko Haram.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan kasar na zanga-zanga ne kan matakin gwamnati na cire tallafin man fetur - suna kira ga gwamnati da ta sake tunani amma ba wai kokarin kifar da ita suke yi ba.

A kasar Uganda, an gudanar da zanga-zanga kan farashin albarkatun man fetur - ba wai don neman kifar da gwamnati ko kawar da shugaban kasa ba.

Irin wadannan bukatun za a iya shawo kansu ne kawai ta hanyar samar da hukumomi - ba wai kawar da shugabanni ko kifar da gwamnatocinsu ba.

Kuma wannan shin ne mataki na gaba da ya kamata a dauka a fagen demokuradiyya a nahiyar Afrika - ba wai bore makamancin na kasashen Larabawa ba.

Karin bayani