Bom ya kashe akalla mutane 24 a Bagadaza

Tashin bom a Iraki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tashin bama-bamai abu ne da ya zama ruwan-dare a Iraki

Rahotanni daga Iraki sun ce tashin bama-bamai ya kashe akalla mutane ashirin da hudu a birnin Bagadaza.

Ga alamu an kai harin ne yayin wata jana'iza a wata unguwa inda 'yan Shi'a da mabiya Sunnah ke cakude.

Wani jami'in kasar Iraki ya ce wani dan kunar-bakin-wake ne ya tashi wata motar da ke makare da abubuwa masu fashewa.

Har yanzu bayanai na ci gaba da shigowa dangane da harin.