An yi harbe-harbe a birnin Kanon Najeriya

Wasu daga cikin mutanen da hare-haren ranar Juma'a suka shafa
Image caption Akalla mutane dari biyu ne suka rasa rayukansu a hare-haren ranar Juma'ar makon da ya gabata

Wadansu rahotanni daga Kano a arewacin Najeriya sun ce jiya da magriba an yi harbe-harbe a unguwar Mandawari da ke tsakiyar birnin.

Mazauna unguwar sun shaidawa BBC cewa an fara harbe-harben ne daura da ofishin ’yan sanda na Mandawarin, an kuma shafe kimanin mintuna arba'in ana jin karar harbe-harben.

Wani mai shago a kusa da inda al’amarin ya faru ya ce ya ji wadansu mutane suna kabbara a lokacin da ake harbe-harben.

Mutumin, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar da cewa an yi harbi da manya da kuma kananan binigogi, sai dai ya ce babu fashewar komai a wajen.

Haka kuma wadansu mutanen da ke wajen sun ce maharan sun je ne a kan babura.

’Yan sandan sun tabbatar da cewa wani kofur ya rasa ransa, yayinda maharan suka gudu suka bar bindiga daya.

Ya zuwa yanzu dai komai ya lafa.

A ranar Juma'ar makon da ya gabata ne aka samu tashin wasu bama-bamai a birnin a gine-ginen jami'an tsaro akalla guda takwas, al’amarin da ya haifar da rudani da tashin hankali a jihar ta Kano.

Kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da suna Boko Haram dai ta dauki nauyin kai hare-haren na ranar Juma’a.

Kusan mutane dari biyu ne hukumomi suka ce sun rasa rayukansu a hare-haren, ban da wadansu daruruwa da suka jikkata, tare da asarar dukiyar da har yanzu ba a san adadinta ba.

Karin bayani