Ministan kudin Kenya, Uhuru Kenyatta ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ministan kudi na kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya yi murabus daga mukaminsa.

Hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayyana cewa, ya kamata ya fuskanci shari'a akan tashe-tashen hankulan da aka yi a kasar, a shekarar 2008.

Sai dai duk da murabus din da ya yi daga ministan kudi, Mr. Kenyata zai ci gaba da kasancewa mataikamakin Firai Ministan kasar, a cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin Shugaban kasar Mwai Kibaki.

Mr. Kenyatta na daga cikin mutane hudu fitattu da kotun duniyar ta ambato za su gurfana a gabanta.