Tashin hankali ya barke a kasar Senegal

Masu zanga-zanaga sun rika kona tayoyi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daruruwan matasa masu zanga-zanaga sun rika kona tayoyi

Tashin hankali ya barke a Dakar, babban birnin kasar Senegal, bayan Kotun Tsarin Mulki ta kasar ta yanke hukuncin cewa Shugaba Abdoulaye Wade zai iya tsayawa takara don neman wa'adin mulki na uku a zaben da za a gudanar a watan gobe.

Kotun ta kuma yi watsi da takarar mawakin nan Youssou N'Dour, a zaben na watan gobe.

Daruruwan matasa masu zanga-zanga ne suka rika kona tayoyi suna kuma jifan 'yan sanda da duwatsu; su kuma 'yan sandan suka mayar da martani da harba hayaki mai sa hawaye.

Tashin hankalin ya barke ne 'yan mintuna kadan bayan da Kotun Tsarin Mulkin ta yanke hukuncin.

Shugaba Wade dai ya yi kira a kawo karshen wannan al'amari wanda ya kira tsageranci, yana mai cewa an kafa dokar ta kayyadewa shugaban kasa wa'adi biyu ne kawai bayan an zabe shi—don haka ba zai yiwu dokar ta yi aiki a kansa ba.

Mawakin nan mai adawa da Shugaba Wade, Youssou N'Dour, ya yi gargadin cewa zaman dardar na karuwa, sannan ya ce zai kalubalanci haramta masa tsayawa takarar da Kotun ta yi.

Wani mazauinin birnin na Dakar, Emmanuel Camara, ya yi gargadin cewa tsugune ba ta kare ba:

“Matsanmu—abin da muke kira rundunonin matsanmu—za su ja daga a kan tituna; sam, ba za mu amince da hukuncin Kotun Tsarin Mulkin ba”.

Karin bayani