'Tsofaffin 'yan tawaye sun rikita Libya'

Daya dag cikin rundunonin juyin-juya-hali na Libya
Image caption Daya daga cikin rundunonin juyin-juya-hali na Libya

Manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwa game da wadansu rundunonin juyin-juya-hali na Libya wadanda ake zargi da haddasa karuwar tashe-tashen hankula da kuma tsare dubban mutane a wadansu boyayyun wurare a kasar.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar ta Libya, Ian Martin, da kuma kwamishiniyar Majalisar mai kula da kare hakkokin bil-Adama, Navi Pillay, su ne suka furta hakan a gaban Kwamitin Sulhu.

Ian Martin ya shaidawa Kwamitin Sulhun cewa akwai kuskure a labarin da aka bayar na ba-ta-kashin da aka yi a Bani Walid tsakanin mutanen garin da kuma dakarun juyin-juya-halin da ke can, wanda aka ce dakarun da ke goyon bayan Kanar Gaddafi ne suka yi yunkurin sake karbe iko da garin.

Sai dai kuma, duk da haka, wannan ya nuna kalubalen da ake fuskanta a yunkurin sasanta magoya bayan Kanar Gaddafi da 'yan tawayen da suka murkushe su.

Mista Martin ya ce ko da yake gwamnatin rikon kwaryar kasar ta yi yunkurin karbe makaman da ke hannun tsofaffin 'yan tawayen, raunin da take da shi ya sa ita kanta tana fafutukar tabbatar da ikonta ne a wani yanayi mai wuyar sha'aniā€”inda rundunonin, dauke da makamai amma kuma babu wani tsari na umurni da hani, suka yawaita.

Ya kuma ce wadannan 'yan bindiga ne suka haddasa munanan tashe-tashen hankula a Tripoli da sauran gruruwa a wannan watan.

Wani batun kuma shi ne na wuraren tsare mutane wadanda ke karkashin ikon rundunonin: tuni dai aka mikawa gwamnatin rikon kwaryar shida daga ciki amma, a cewar Navi Pillay, akwai wadansu akalla guda sittin wadanda ke dauke da fursunoni dubu takwas da dari biyar, akasarinsu mutanen da ake zargin magoya bayan Kanar Gaddafi ne. Da dama daga cikinsu kuma 'yan asalin Afirka kudu da Sahara ne.

Daga ita har Mista Martin sun yi kira ga hukumomi su karbe wadannan gidajen yari su kuma yi nazarin laifuffukan da fursunonin suka aikata kamar yadda doka ta tanada.