Amurka ta ce za ta rage yawan sojojinta

Leon Panetta
Image caption Sakataren Tsaron Amurka, Leon Panetta

Gwamnatin Amurka ta bayyana wani shiri na rage kudaden da take kashewa a kan rundunonin sojinta a shekaru goma masu zuwa.

Sakataren Tsaro Leon Panetta ne ya yi karin haske a kan biliyoyin dalolin da za a rage a cikin kudaden da ake kashewa a kan rundunonin sojin, yana cewa lokaci ya yi da rawa za ta sauya bayan an kwashe shekaru goma ana yaki, ana kuma fadada kasafin kudin bangaren tsaro.

A karkashin shirin dai, za a rage yawan rundunar sojin kasa da sojoji dubu tamanin, yayin da sojojin ruwa dubu ashirin za su yi sallama da wuraren aikinsu.

A kasafin kudin kasar na badi, an rage kudaden da aka warewa bangaren tsaro da dala biliyan talatin da uku, sannan kuma za a jinkirta wani shiri na kera sababbin jiragen yaki na sama da masu tafiya a karkashin ruwa.

Sai dai kuma za a kara yawan kudaden da ake kashewa a kan dakaru na musamman, ciki har da dakarun kundumbala wadanda za a koyawa harsuna da al'adun kasashen waje, da kuma samar da jiragen sama masu sarrafa kansu.

Sakataren tsaron ya ce wannan ba kawai rage kashe kudi ba ne, wata dama ce ta sauya alkibilar manufofin tsaro na Amurka daga Iraki da Afghanistan zuwa ga Gabas ta Tsakiya da yankin Pacific da kuma intanet.

“A zahiri rundunar sojin za ta kankance, akwai kuma hadarin da ke tattare da hakan; sai dai ina ganin mun magance hadarin saboda irin rundunar da za mu samar da kuma zafin namanta zai ba mu dama fuskantar duk wata barazana a karni na ashirin da daya”, in ji Mista Panetta.

Sai dai 'yan jam'iyyar Republican sun yi Allah-wadai da shirin saboda, a cewarsu, Amurka ba ta san irin kalubalen da za ta fuskanta ba nan gaba.

Karin bayani