An kashe mutane goma sha biyar a wani fashi a Zamfara

Hakkin mallakar hoto Aliyu

Rahotanni daga Jahar Zamfara sun ce akalla mutane goma sha biyar ne suka mutu lokacinda wasu da ake jin 'yan fashi ne suka budewa motar da suke tafiya aciki wuta. Kwamishinan watsa labarai na jihar ya shaidawa BBC cewar haka ma akwai wasu da suka samu raunuka a harin kuma wasu da dama ba'a san inda suke ba. Lamarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Shamusalle na jihar ta Zamfara wanda ke kusa da iyakar jahar da makwabciyar Jihar Katsina.