Soji sun harbe mutane 11 a Maiduguri da suke zargin 'yan Boko Haram ne

Wasu mutane da aka kashe a lokacin harin Boko Haram
Image caption Mutane suna ci gaba da rasa rayukansu

A birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau din nan, rundunar hadin gwiwa ta tsaro wato JTF ta ce ta harbe mutane goma sha daya, wadanda take zargin 'yan kungiyar nan ne na Jama'atul Ahalil sunnah Lidawati wal jihad, wadda aka fi sanni da Boko Haram.

Kakakin Rudunar tsaron Leftanal Kanal, Muhammed Hassan, ya tabbatarwa BBC aukuwar lamarin.

Ya ce jami'an tsaron sun harbe su ne a lokacin musayar wuta bayan rundunar ta kafa shigayen binciken ababen hawa a cikin tsakiyar birnin Maiduguri.

Ko a jiya da maraice ma dai kungiyar ta Boko Haram ta kai hari a unguwar Mandawari ta birnin Kano, inda ta kashe dansanda guda.

Kana mako daya bayan a Kanon, ta hare-haren da suka kai ga rasuwar mutane fiye da dari da tamanin.