Gwamnatin Afghanistan za ta tattauna da Taleban a Sa'udiya

Shugaba Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ko a wannan karon Taleban za ta amsa kiransa?

BBC ta samu labarin cewa gwamnatin Afghanistan na shirin ganawa da kungiyar Taliban a kasar Saudiyya cikin 'yan makwanni masu zuwa.

Tattaunawar, wadda ita ce irinta ta farko, wani muhimmin abu ne a kokarin da ake yi na samun hanyar warware rikicin Afghanistan.

Abu na baya-bayan nan da aka maida hankali a kai shi ne na kokarin da Amurka ke yi domin ganawa da 'yan Taliban din, wadanda ke son kafa wani ofishi a Qatar:

Wakiliyar BBC ta ce shugaba Hamd Karzai ya ji haushin kokarin da Amurka da Qatar ke yi na tattaunawa da Taliban ba tare da tuntubar gwamnatinsa ba.

Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai, ya ce ya kamata Afghanistan ce za ta jagoranci tattaunawar zaman lafiyar, sai dai a baya kungiyar Taliban ta gwasale gwamnatinsa, wadda take dauka a matsayin haramtacciya.

Karin bayani