Austrailian Open: Djokovic ya doke Nadal a wasan karshe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Djokovic ya doke Nadal, a haduwarsu sau shida a jere

Novak Djokovic ya karfafa matsayinsa a na daya a fagen Tennis a duniya bayan da ya doke Rafeal Nadal a wasan karshe a gasar Australian Open.

Djokovic ya doke Nadal ne na ci uku da biyu a wasanni biyar da su ka buga wanda ya kai kusan sa'a shida ana fafatawa.

Wasan na karshe ya shiga tarihi, saboda shine aka taba bugawa na tsawon lokacin da ya kai sa'a biyar da minti hamsin da uku a gasar ta Austrailian Open.

Djokovic, dai ya doke Nadal a jere sau shida a haduwar da suka yi a gasa dabam-dabam.