Shugaban Yemen ya isa Amurka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Ali Abdallah Saleh

Shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen ya isa Amurka inda ya ce yana kasar ne don a duba lafiyarsa.

Ya kara da cewa zai koma gida da zarar likitoci sun sallameshi.

Ficewar Shugaba Saleh daga kasar a wannan makon, ita ce alama karara da ke nuna cewa zai mutunta yarjejeniyar barin mulkin da ya amince da ita a bara, bayan anyi watanni ana zanga-zangar kin-jinin gwamnatinsa.

Ziyarar tana da sarkakiya sosai ga hukumomin Amurka, saboda bakon nasu ya bayar da hadin kai sosai wajen yaki da ta'addanci.

Amma kuma ba za su so a yi musu kallon wadanda suke bayar da mafaka ga mai mulkin kama-karya da ya yi amfani da karfin tsiya wajen murkeshe mazu zanga-zanga ba.