BBC navigation

An yankewa Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa

An sabunta: 30 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 16:22 GMT

An dai shafe shekara-da-shekaru ana gudanar da wannan shari'a

A Najeriya wata kotun daukaka kara a jihar Legas ta yanke wa tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha hukucin kisa ta hanyar rataya sakamakon kisan matar marigayi MKO Abiola.

Mai shari'a Mojisola Dada ta ce ya kamata a rataye Majar Hamza Al-Mustapha, sakamakon samunsa da hannu a shirya kisan uwargidan shahararren dan kasuwa kuma dan siyasa marigayi Moshood Abiola.

An dai shafe shekara-da-shekaru ana gudanar da wannan shari'a - wacce ta ja hankalin jama'a a kasar.

Muna dauke da karin bayani.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.