An kashe fararan hula biyu a Kano

Harin da wasu 'yan bindiga suka kai a Kano Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin da wasu 'yan bindiga suka kai a Kano

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan ofisoshin 'yan sanda biyu a birnin Kano da ke Arewacin Najeriya cikin sa'o'i ashirin da hudun da suka gabata.

An jefa bam a ofishin yan sanda na Na'ibawa ranar Lahadi da daddare, sannan aka kashe fararen hula biyu a musayar wutar da ta biyo baya.

Da sanyin safiyar yau ne kuma wasu yan bindigar a cikin motar safa suka bude wuta kan ofishin 'yan sanda na unguwar Mandawari a tsakiyar birnin na Kano - kuma shi ne karo na biyu da aka kaiwa ofishin hari cikin kwana biyu.

Birnin Kano ya fuskanci munanan hare-hare da kungiyar Boko Haram ta kai a Najeriya.

Kusan mutane 200 ne aka kashe a hare-haren bama-baman da kungiyar ta kai a birnin kwanaki goman da suka wuce.

Karin bayani