Kotun Kolin Senegal ta yi watsi da bukatar 'yan adawa

Image caption Abdoulaye Wade

Kotun kolin Senegal ta yi watsi da bukatar 'yan adawa ta hana shugaban kasar Abdoulaye Wade, shiga takarar shugabancin kasar a karo na uku, tana mai tabbatar da cewa shugaban zai iya tsayawa.

Kotun ta ki amincewa da hujjar 'yan adawa ta cewa tsarin mulkin kasar ya ce wa'adin mulki biyu ne kawai ake yi, tana mai cewa dokar bata shafi shugaba Wade ba, saboda bayan an zabe shi ne dokar ta fara aiki.

Kotun ta kuma tabbatar da rashin cancantar takarar mawakin nan Yoousou Ndor.

Sai dai a martanin da ya mayar, Mr Ndor ya yi watsi da hukuncin yana mai bayyana shi da cewa wani juyin mulki ne kawai:

'' An ci mutuncin Senegal, an lalata kimar da take da ita.An tabbatar da juyin mulki da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan.An kassara tsarin mulkin dimokaradiyyar da aka kwashe shekaru 52 ana amfani da shi''.

Ya yi kira ga 'yan kasar da kuma kasashen duniya da su hada karfi da karfe wajen ceto ta daga wargajewa.

Karin bayani