Kasashen Turai na taro a kan tattalin arzikinsu

Image caption Tutar kungiyar Tarayyar Turai

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai za su yi taro a ranar Litinin a birnin Brussels a kan matsalolin tattalin arziki da nahiyar ke fama da su.

Taron zai mayar da hankali ne akan yarjejeniyar raya tattalin arziki da ta tanadi tsauraran matakan kasafin kudi.

Ana kuma sa ran za a tattauna akan matsalar bashin kasar Girka.

Rahotanni sun nuna cewa watakila a cimma yarjejeniya da wasu bankuna akan su yafe mata wani bangare na bashin da ake bin ta.