Kotu ta wanke Bankole da Nafada

Kotu ta wanke Bankole da Nafada Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lauyoyin EFCC sun ce ba su yarda da hukuncin ba

Wata babbar kotu a Najeriya ta wanke tsohon Kakakin majalisar wakilan kasar, Hon Dimeji Bankole da mataimakinsa Hon Usman Bayero Nafada daga zargin aikata laifuka 17 da suka shafi cin hanci da rashawa.

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ce, ta tuhumce su da aikata laifuka guda goma sha bakwai, da ta ce sun sabawa tsarin mulkin kasar.

Laifukan sun shafi karbar rancen sama da naira biliyon arba'in da sunan majalisar wakilai tare da sarrafa kudin ba bisa ka'ida ba.

Kotun ta ce masu karar sun gaza wajen gabatar da shaidar da za ta gamsar cewa wadanda ake zargin sun aikata lafukan da ake zarginsu da aikatawa.

To sai dai Lauyan da ke tsayawa wa hukumar EFCC Festun Kiyamo ya ce bai gamsu da hukuncin kotun ba.

A bara ne aka kama Dimeji Bankole da kuma Bayero Nafada sannan aka gurfanar da su a gaban kotu jim kadan bayan sun kammala aikinsu na Majalisa.

Karin bayani