Kasashen Turai sun amince da yarjejeniya kan harkokin kudi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu shugabannin kasashen Turai

Kasashe 25 daga cikin 27 na Tarayyar Turai sun amince su rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta shafi tsara kudade, domin kauce wa sake fadawa matsalar bashi a nan gaba.

Yarjejeniyar za ta hukunta duk wata kasa da ta sabawa adadin bashin da za ta iya ciyowa don aiwatar da kasafin kudinta.

Kazalika kasashen za su sanya yarjejeniyar a cikin dokokinsu don tabbatar da daidaiton kasafin kudi.

Jamhuriyar Czech ta bi sahun Burtaniya wajen kin shiga yarjejeniyar, wadda ta tanaji wasu sharudda masu tsauri kan kasafin kudi.

Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron, ya ce kasar za ta sanya ido sosai don ganin sabuwar yarjejerniyar ba ta yi tasiri a kasuwar kudi ta bai-daya ba.