'Pakistan na goyon bayan 'yan Taliban'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan kungiyar Taliban

BBC ta samu wani rahoton asiri na kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan da ke cewa har yanzu kungiyar Taliban na samun taimako kai tsaye daga Pakistan.

Rahoton ya ce kungiyar na samun goyon baya sosai tsakankanin 'yan kasar ta Afghanistan.

An gina rahoton ne a kan bayanan da aka tatsa har guda dubu ashirin da bakwai daga 'yan Taliban da al-Qaeda da ma wasu.

Rahoton ya ce Pakistan na ci gaba da kada akalar shugabannin Taliban, kuma ta san inda suke.

Ya kuma yi zargin cewa jami'an tsaron Afghanistan na sayar da makamai ga kungiyoyin masu tayar da kayar baya.

Sojojin kasashen yamma da ke Afghanistan sun ki cewa uffan a kan rahoton.

Karin bayani