Mitt Romney ya lashe zaben Florida

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mitt Romney

Masu kada kuri'a a jihar Florida sun zabi Mitt Romney, a matsayin dan takarar jam'iyyar Republican da suke son ya kalubalanci shugaba Obama a zaben shugaban kasa na gaba.

A yayin da ake dab da kammala kidaya dukkan kuri'un da aka kada, a fili ta ke cewa Mr Romney ne ya lashe zaben da kashi 46 cikin dari na kuri'un da aka kada, inda abokin hamayyarsa Newt Gingrich ya samu kashi 32 cikin dari.

Mr Romney ya shaidawa magoya bayansa cewa takara ta yi zafi tsakaninsa da Mr Gingrich, yana mai cewa dole a samu irin wannan takun-saka idan ana zaben fidda gwani.

Sai dai wannan nasara ba ta zo masa cikin sauki ba, domin kuwa sai da ya kashe akalla dala miliyan 16, sannan ya kashe pam miliyan goma wajen baiwa gidajen talabijin din Florida tallace-tallace game da takararsa.

Akasarin tallace-tallace guda dubu goma 13 da ya bayar, sun yi suka ne kan abokin hamayyarsa, Newt Gingrich.

Mr Gingrich dai ya yi watsi da rahotannin da ke cewa watakila ya janye daga yin takarar, yana mai cewa zai yi takara a zaben da za a gudanar a dukkan jihohi arba'in da shida da suka rage.