Ana ci gaba da muhawara a kan Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bashar al-assad

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da muhawara game da wani kudiri kan kasar Syria, wanda ke kira ga Shugaba Assad da ya mika ragamar mulki ga wani mataimakinsa.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce akwai kwararan shaidu da ke nuna cewa dakarun gwamnatin Syria su ne ke fara kai kusan dukkan hare haren da suka yi sanadiyar kashe fararen hula.

Jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya, Bashar Ja'afari, ya ce a kyale kasarsa ta magance matsalarta ta cikin gida:

''Kishin kasar Syria na adawa da duk wani tsoma baki daga waje'', yana kuma jaddada 'yancin kasar, da kare mutuncinta.

Kasar Qatar da ke yankin Gulf ta bukaci kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki wani mataki, amma jakadan kasar Rasha ya ce Majalisar ba ta da ikon tilasta hanyar da za a bi a warware rikicin kasar ta Syria.