Wasu 'yan Biritaniya sun amsa laifin shirin dana bamabamai

London Stock Exchange Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Inda aka yi niyyar kai hari

Wasu 'yan Biritaniya hudu sun amsa cewa sun yi kokarin dana bam a kasuwar hannayen jari ta birnin London.

Mutanen 'yan Biritaniya, amma 'yan asalin kasashen Bangladesh da Pakistan, suna cikin wasu mutane tara ne da suka amsa yunkurin aikata laifukan ta'addanci da dama.

Mutanen, wadanda suka tasirantu da koyarwar wani malamin addini dan kasar Yemen, Anwar Al Awlaki, an kama su ne a watan Disamban shekara ta 2010 kafin su kai harin - ta hanyar dana bam din a wani bandaki da ke kasuwar hannayen jarin ta London.

Masu gabatar da kara sun ce mutanen sun shirya kai hare-hare a wurare da dama ciki harda majalisar dokokin Burtaniya - makamancin wanda aka kai a birnin Mumbai na India wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 170 a shekara ta 2008.

Matasan na London da kuma na garin Cardiff suna tattaunawa da wata tawagar dake Stoke-On-Trent wadanda su kuma suka yanke shawarar dasa bambamai a wasu mashayu.

Suna gabda fuskantar shari'a sai suka amsa laifi bayan da alkalin ya ce idan har shugaban kitsa harin, Mohammed Chowdhury, ya amsa laifinsa, to a maimakon shafe shekaru goma sha uku da rabi a gidan yari, watakila ya shafe shekaru shida ne kawai.

Karin bayani