Dalibi a Senegal ya rasu sakamakon zanga-zanga

masu zanga zanga a Senegal Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption masu zanga zanga a Senegal

A kasar Senegal, zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar ta dauki wani sabon salo, inda dalibai suka shige ta kain da nain.

Daliban dai sun harzuka ne bayanda jamian tsaro suka halaka daya daga cikinsu a lokacinda suke gudanar da zanga zangar a jiya.

Tun bayanda kotun tsarin mulkin kasar ta baiwa shugaba Abdullahi Wade damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar ne dai ake ta samun zanga zanga a kasar.

Wani mutum guda ma ya rasa ransa a farkon mako a kasar, lokacin tashin hankali na baya-bayan nan tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a Dakar, babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce wata motar 'yan sanda ce ta bi ta kan mutumin, a lokacin zanga-zangar nuna adawa da shawarar shugaba Abdoulaye Wade ta neman wa'adin mulki karo na uku.

'Yan sanda sun harba barkonin tsohuwa domin tarwatsa wani gangami na masu adawa da hukuncin kotun da ya baiwa Mr Wade damar yin tazarce, ya kuma haramta wa wasu mutanen tsayawa takara.

Amurka ta yi gargadin cewa wannan hukunci zai iya illa ga kimar da aka dade ana kallon kasar ta Senegal da ita ta fuskar dimokradiyya da ma zaman lafiyarta.

Haramtacciyar Zanga-zanga

A baya dai Gwamnatin kasar Senegal ta ce zanga-zangar da 'yan adawa suka shirya gudanarwa a kasar haramtacciya ce, sai dai 'yan adawar sun ce ba gudu ba ja da baya.

Kungiyoyin 'yan adawar - da aka fi sani da M23 - suna adawa ne da shirin shugaba Abdullahi Wad na tsayawa takara karo na uku.

Daraktan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International a Senegal Seydi Gasama, ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar a samu tashin hankali idan 'yan sanda suka yi kokarin hana zanga-zangar.

"Damuwarmu ita ce za a iya jikkata mutane ko ma a kashe wasu, idan 'yan sanda suka yi tawo muga da masu zanga-zangar kamar yadda ta faru a jiya".

Shugaban Cibiyar Raya Demokuradiyya ta Najeriya Dr Jibril Ibrahim wanda ke halartar zanga-zangar a Senegal, ya shaida wa BBC cewa ya je kasar ne domin tabbatar da tsarin demokuradiyya.

Masu zanga-zangar na adawa ne da hukuncin kotun koli wanda ya baiwa shugaba Wad dan shekaru 85 damar tsayawa amma aka hana wasu.

Amurka ta yi gargadin cewa hukuncin zai zubar da kimar da kasar take da ita a fannin demokuradiyya.

Za a gudanar da zabe ne a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Karin bayani