Jaridar Ukraine ta kira 'yan Afrika da Larabawa birai

Hakkin mallakar hoto All Sports
Image caption Kasar Ukraine dai na fama da matsalar wariyar launin fata

Masu fafutukar kawar da wariyar al'umma a Ukraine sun yi kira ga shugaban kasar Victor Yanukovych da ya kawar da wariyar al'umma da kyama daga kasar.

Wannan ya biyo bayan wani labari da wata jarida a garin Ternopil, ta buga game da wata hayaniya da ta shiga tsakanin dalibai 'yan Afrika da Larabawa akan wata budurwa, inda Jaridar ta kwatanta wadannan dalibai da birai.

Jaridar mai suna Ternopilska Hazeta, ta ce haka ta ga ya kamata ta bada labarin wata hayaniya da ta tashi a Mashaya tsakanin 'yan Afrika da Larabawa dalibai.

A shafin farko jaridar an rubuta kuru kuru cewa 'an zubar da jini baki' yayin da 'yan Afrika da Larabawa su ka kara akan 'yan mata.

Wariyar launin fata

Wannan sako na cin zarafi an kara fadada shi inda aka nuno hoton wasu Birrai guda biyu kewaye da wata yarinya mai karancin suttura a jikinta, da kuma wani babban hoto na wasu 'yan Afrika dalibai na shan barasa.

Wannan jarida dai ta kare wannan labari nata, inda ta ce tana so ne kawai ta nuna cewa duk wani wanda ke bige ka iya kasancewa tamkar Biri.

Wannan bayani bai kawar da halin takaicin da dalibai 'yan kasashen waje suka shiga ba, a saboda haka ne Mohammed Sisey shugaban dalibai 'yan Afrika a Ukraine ya shaidawa manema labarai a Ukraine cewa wannan irin nuna banbancin launin fata da wariya kirikiri bai dace da zamantakewar kasar da kai ya waye ba, ya kuma nemi hukumomi da su sanya baki.

Mahukunta a Ternopil dai sun ce suna gudanar da bincike don ganin ko akwai bukatar kaddamar da matakin shari'a bisa wannan jarida, kamar yadda wata mai magana da yawun hukumomin Lesia Dolishnia ta ce.

A bisa alkaluman da Ma'aikatar Ilimi ta kasar ta bayar, dalibai 'yan kasashen waje sama da 400,000 wadanda suka je kasar daga kasashe 130 ne dai a yanzu ke karatu a Ukraine, inda ake da kimanin dalibai 2,000 a garin Ternopil.

Dalibai da dama daga Afrika da kasashen Asiya na zuwa Ukraine karatu ne don saboda rangwamen kudin makaranta.

Yanzu al'amurra na sauyawa saboda kuka da daliban ke yi na nuna kyama da wariya daga bangaren jama'ar gari.

Majalisa Ternopil ta musanta

Majalisar garin Ternopil dai ta yi azamar musanta wannan zargi na matukar nuna wariya inda a wani shafinta na yanar Gizo ta ce yawan dalibai 'yan kasashen waje na karuwa ne a cikin shekaru 10 da suka gabata amma ba raguwa saboda wariya.

A wani jin ba'asin jama'a Babor James Aganren, shugaban daliban Najeriya a garin na Ternopil, ya bukaci Jaridar da ta rubuta neman afuwa a shafinta na farko, ya kuma ce ya kamata a hukunta editan wannan Jarida.

Jaridar dai ta buga wannan neman afuwa, inda ta ce ta yi takaicin yadda abinda ta rubuta ya dora alamar tambaya mai dangantaka da wariyar alumma ga jaridar, garin Ternopil da kuma Ukraine baki daya.

Wannan batu dai ya kara kunyata Ukraine a lokacin da kasar ke kokarin inganta mutuncinta a idon duniya, daf da lokacin fara gasar kwallon kafa ta kasashen Turai, gasar da Ukraine ke daukar nauyi tare da Poland.