Boko Haram ta ce ba Abul Qaqa ne jami'an tsaro suka cabke ba

boko haram Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

A Najeriya wani mutum da ya ke ikirarin cewa shi ne mai magana da yawun kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram Abu Qaqa, ya yi magana da manema labarai a Maiduguri , inda ya shaida musu cewa ba shi jami'an tsaro suka kama ba, wanda aka kama din sunansa Abu Darda jagoran sashen wayar da kan al'umma na kungiyar ta Boko Haram.

Bayanai dai sun nuna cewa jami'an tsaro na ci gaba da yin tambayoyi ga mutumin da suka kama a ranar Larabar da ta gabata inda wata majiya ta hukumar leken asirin kasar ta ce, Abu Qaqa ne mai magana da yawun kungiyar.

Mutumin wanda ya yi magana da manema labarai ta wayar tarho, ya yi ikirarin cewa shi ne Abu Qaqa sabanin bayanan da wasu jami'an tsaro na SSS suka tsegunta wa manema labarai cewa sun kama shi.

Sai dai ya tabbatar da cewa wanda jam'ian tsaron suka kama sunansa Abu Darda kuma shi ne shugaban lajna wato sashen wayar da kan al'umma na kungiyar ta Boko Haram.

'Kofar rago'

Mutumin ya kuma yi zargin cewar kamen da jami'an tsaro suka yi yaudara ce tsagwaronta aka yiwa kungiyar, domin sun yi kiran tattaunawa amma suna aikata sabanin hakan.

Ya ce sun aika Abu Darda ne zuwa Kaduna domin ya tuntubi wasu jami'an gwamnati a kan batun na tattaunawa da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kiran a yi, kuma ya fara tattaunawa da su, amma kuma suna zargin su jami'an gwamnatin ne suka umarci jami'an tsaro su bi diddiginsa su kama shi.

Ya kuma kara da cewa, a da, sun shirya cewa, bayan tattaunawar Abu Darda da jami'an gwamnati, za su tura mutane biyar da za su wakilce su.

Sai dai BBC ba ta iya tantance sahihancin wannan ikirari ba domin wasu majiyoyi sun nuna shakku akan muryar da ta yi magana da yan jaridar a jiya, inda suka nuna cewa muryar ta sha bamban da wadda ta saba kiran 'yan jarida ta yi ikirarin kai hare-hare da dama.

Majiyoyin sun kuma bayyana cewa, an jima ana nuna shakku, ko lakabin Abu Darda da Abu Qaqa duk na mutum daya ne.

Wasu abubuwa da suka fito fili dai sune, ko ma wanene Jami'an tsaro suke rike da shi, to mutum ne da ke da babban mukami a cikin Kungiyar ta Boko Haram, ganin irin matsayin da kungiyar ta bayyana shi, da cewar babban Jami'i ne mai kula da wayar da kan al'umma na Kungiyar.

Mai yiwuwa ma kuma mutum ne da ya fi Kakakin Kungiyar matsayi a cikin tsarin shugabanci na wannan kungiya.

Haka kuma a karo na farko, daga abubuwan da ke cikin wannan sanarwa, akwai alamun a shirye kungiyar ta ke, duk kuwa da irin bayanan da ta ke fitarwa a baya, cewar zata iya karbar goron gayattar shiga tattaunawa tare da gwamnati, ganin cewa ita da kanta kungiyar na ikrarin cewar wannan babban jamii da aka kama ya je Kaduna ne domin tattauna da wasu jamia'n gwamnati.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin Nigeria, ko kuma hukumar leken asiri ta Nigeria, dangane da wannan sabon ikrari na kungiyar ta Boko Haram, cewar mutumin da aka kama ba kakakin kungiyar ba ne, jagora ne na sashen wayar da kan jamaa.

A ranar Laraba ne dai wani jami'in hukumar leken asiri ta kasa SSS ya shaida wa manema labarai cewa sun kama mai magana da yawun kungiyar ta Boko Haram Abu Qaqa, ta hanyar bin diddigin signal din da wayar salularsa ke fitarwa.

Karin bayani