Tankiya tsakanin Isra'ila da Iran

Ayatollah Ali Khamenei Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ayatollah Ali Khamenei

Jagoran addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na kai wa kasarsa hari saboda shirinta na nukiliya, zai gamu da murtani mai tsauri daga kasar.

Ayatollah Khamenei ya ce, yin barazana ga Iran ko kuma kai ma ta hari, zai cutar da Amurka ne kawai.

Ya ce: "Suna yi mana barazana a kai a kai, wadda ta hada da yiwuwar kawo mana hari. Yaki zai yiwa Amurka illa sau 10 fiye da illar da zai yiwa Iran".

Jawabin nasa dai ya zo ne kwana daya bayan da ministan tsaron Isra'ila, Ehud Barak, ya fada wa wani taro kan harkar tsaro cewa, lokaci yana kurewa game da batun dakatar da shirin nukiliya na Iran.

Tuni dai jami'an gwamnatin Amurka, ciki har da Sakataren tsaro Leon Panetta, suka nuna damuwar cewa Isra'ila na tunanin kai hari a kan kasar ta Iran.

Karin bayani