Kisan da cutar malairia ke yi ya ribanya sau biyu

cutar malairia Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption cutar malairia

Wani sabon nazari da aka yi ya nuna cewa, cutar zazzabin cizon sauro, wato Malaria na hallaka yawan jama'ar da ya wuce yadda ake zato a baya har sau biyu.

Masana kimiyya a Amurka da kuma Australia sun ce, fiye da mutane miliyan guda da dubu dari biyu ne cutar ta Malaria ta hallaka a shekara ta 2010, kuma wannan adadi ya rubanya alkaluman hukumar lafiya ta duniya, wato WHO.

Manazartan sun ce sabon nazarin wanda ya hada da mutanenda a baya aka dauka cewa wata cutar ce ta halaka su, ta kai abinda mujallar The Lancet ta bayyana da cewa, adadi mai tada hankali.

Karin bayani